Saturday, June 13, 2026
HomeLabarai‎An Gano Ƙasusuwan Dinosaur Mai Shekaru Miliyan 95 a Nijar

‎An Gano Ƙasusuwan Dinosaur Mai Shekaru Miliyan 95 a Nijar

‎Wata tawagar masana kimiyya ta samu nasarar gano ƙasusuwan wani nau’in dinosaur da ya ɓace a yankin hamadar Sahara da ke cikin Jamhuriyar Nijar. Masanan sun bayyana cewa wannan halitta na daga cikin jinsin Spinosaurus mirabilis, wadda ta rayu kusan shekaru miliyan 95 da suka gabata.

‎Masu binciken sun ce wannan ganowa na daga cikin manyan nasarori a fannin ilimin tarihi da kimiyyar halittu, domin ta taimaka wajen ƙara fahimtar yadda manyan dabbobin da suka ɓace suka rayu a Afirka a zamanin da.

‎Rahotan Tashar Geo News ya nuna cewa Spinosaurus mirabilis dabba ce mai girma wadda ke rayuwa a kusa da ruwa, tana cin kifaye, kuma yanayin ƙasusuwan da aka gano ya nuna cewa yankin Sahara a wancan lokaci yana da ruwa da ciyayi.

‎Masana sun jaddada cewa wannan bincike zai buɗe sabbin ƙofofi na bincike tare da jawo hankalin duniya kan muhimman kayan tarihi da ke ƙasashen Afirka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments