Thursday, October 29, 2026
HomeLabaraiZan Bibiyi Mukarrabaina Kan Gudummuwar da Za Su Bada Ga Rumfunan Zabensu...

Zan Bibiyi Mukarrabaina Kan Gudummuwar da Za Su Bada Ga Rumfunan Zabensu a 2027– Radda

A daide lokacin da ake kaddamar da yakin Neman Zaben Tinubu/Dikko a karamar hukumar Funtua, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa zai sa’ido a Kananan Hukumomi, Mazabu da kuma Rumfunan zabe tare da bibiyar duk abubuwan da ke wakana ga mukarrabansa dake jam’iyyar APC gameda gudummuwar da suka bada a zaben jam’iyyar APC a 2027.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Gwamnan ya bayyana haka a lokacin da yake karama ‘ya’yan jam’iyyar APC da mukarrabansa kwarin guiwa na zaben 2027, a lokacin da ya kaddamar da yakin Neman Zaben sa a Funtua, ranar Laraba 28 ga watan Oktoba 2026.

Dikko, ya ce suna da yakinin za su lashe zabe mai zuwa duba da irin ayyukan da suka shimfiɗawa al’ummar jihar Katsina, kuma alƙawarin da suka dauka suna ci gaba da cikawa.

Haka kuma, ya buƙaci al’ummar jihar da su sake zaɓensa a karo na biyu, domin ya ci gaba da ayyukan raya ƙasa da ya fara tunda farko.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gudanar da ayyuka sama da 1,000 a shiyyar Funtua, inda ya yi karin haske da cewa, ya san ko bayan ba su nan za a rinka tunawa da abubuwan alkhairin da suka yi.

Tun da farko, Gwamna Radda ya kai ziyara gidan Hakimin Funtua, Sarkin Maska, kafin daga bisani ya zarce zuwa filin wasa na Samaila Isah da ke Funtua, inda dubban jama’a suka tarbe shi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments