Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wani mutum mai shekaru 30 da haihuwa bisa zargin sayar da jaririn ‘yar uwarsa mai wata daya kacal kan kudi Naira miliyan biyu. Ana zargin mutumin, mazaunin yankin Igbogbo a karamar hukumar Ikorodu, da sayar da jaririn ne domin samun kudin binne mahaifiyarsu da ta rasu.
Kafar Jarida Radio ta ruwaito cewa mahaifiyar jaririn ce ta kai korafi ga ‘yan sanda bayan faruwar lamarin, wanda ya kai ga kama wanda ake zargin. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olohundare Jimoh, ya bayar da umarnin mika lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na jihar (SCID) da ke Panti domin zurfafa bincike.
Mutumin ya amsa zargin inda ya danganta aikata hakan da tsananin talauci, yana mai cewa ya hadu da matar da ta sayi jaririn ne ta shafin Facebook, sannan wani mutum ya karbi jaririn a Mile 2 bayan an tura masa kudin. Ya ce ya bai wa ‘yar’uwarsa Naira 500,000 daga cikin kudin, amma daga baya ta musanta amincewa da sayar da jaririn tare da kai karar sa ga ‘yan sanda, yayin da jami’ai suka ce za a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike.
