Danmajalisar Tarayya Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Dutsinma da Kurfi, Hon. Aminu Kurfi Balele Ɗan-Arewa ya kai ziyarar girmamawa da godiya ga fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote, a gidansa da ke birnin Legas.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, a yayin ziyarar da ya kai a ranar Litinin, Hon. Aminu Kurfi Balele Ɗan-Arewa ya yaba wa Alhaji Aliko Dangote bisa tsawaita wa’adin sayar da hannun jari a matatar man fetur ta Dangote (Dangote Refinery), matakin da zai ba ƙarin mutane damar shiga cikin harkar zuba jari a matatar.
Ya bayyana cewa wannan mataki zai faɗaɗa damar ‘yan Najeriya na mallakar hannun jari a cikin wannan gagarumin jari, tare da ba su damar zama masu ruwa da tsaki a wani muhimmin kamfani da ke cikin tattalin arzikin ƙasar.
Haka kuma, ziyarar ta ba shi damar bayyana goyon bayansa da nuna godiya ga hangen nesa, jajircewa da ƙudurin Alhaji Aliko Dangote wajen samar da damarmakin da za su ƙarfafa shigar jama’a cikin kasuwar hannayen jari ta Najeriya.
Hon. Aminu Kurfi Balele Ɗan-Arewa ya kuma taya Alhaji Aliko Dangote murnar wannan gagarumar nasara, tare da yi masa fatan samun ƙarin nasarori yayin da wannan shiri ke ci gaba.
A cewarsa, wannan mataki na daga cikin abubuwan da za su iya buɗe sabbin damarmakin zuba jari ga ‘yan Najeriya, ƙarfafa harkokin kasuwanci da kuma bayar da gudummawa ga bunƙasar tattalin arzikin ƙasa.
