Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, ya ce ya kamata al’ummar Katsina su san cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu dan uwansu ne na jini domin Dan Asalin jihar Katsina de don haka su sake zabensa karo na biyu a shekarar 2027, inda ya jaddada wa al’ummar Katsinawa cewa, ya yi kyawawan zama na gaskiya tun siyasa Shehu Musa ‘Yara’dua.
Ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da tsofaffin ‘Yantakara a jam’iyyar APC, waɗanda suka nemi tikitin takararar ɗanmajalisar Tarayya da na dokokin jihar Katsina da shugabannin Kananan Hukumomi da Kansiloli da wakilan ƙungiyoyin siyasa daban-daban a ƙananan hukumomi 34 na Jihar Katsina, domin neman goyan bayan su don tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Malam Dikko Umaru Radda a 2027.
An gudanar da ganawar ne a ranar Juma’a, 2 ga watan Oktoba, 2026, a birnin Katsina, inda aka tattauna kan muhimmancin haɗin kai, tare da tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
A yayin ziyarar, Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya kuma jagoranci buɗe sabbin ofisoshin ƙungiyoyin siyasa guda biyu a Jihar Katsina.
Da yake jawabi a wajen taron, Ibrahim Masari ya jaddada muhimmancin haɗin kai da tsari wajen gudanar da harkokin siyasa, tare da kira ga masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC da su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai tare da tallafa wa jam’iyyar daga sama har ƙasa.
Tunda farko, Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya yaba wa yunƙuri da tsofafaffin yantakarar suke yi na nasarar jam’iyyar a 2027, yana mai bayyana haɗin kai da ci gaba da kasancewa cikin jam’iyya a matsayin muhimman abubuwa wajen gina tsarin siyasa mai ɗorewa.
Kazalika, ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Katsina da ma kasa baki daya da su kasance sun sake zaben jam’iyyar APC tun daga sama har kasa domin ci gaba da raya kasa.
Ganawar ta kasance wata dama ta musayar ra’ayoyi tsakanin masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar, inda aka mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin kai, hulɗa da fahimtar juna tsakanin ƙungiyoyin siyasa da sauran masu ruwa da tsaki.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, bikin buɗe ofisoshin ya samu halartar Ministan Gidaje da Raya Birane, Injiniya Muttaka Rabe Darma; Alhaji Labiru Musa Bakori, ɗan Majalisar Dokokin Jihar Katsina; Barrister Murtala Aliyu Kankia; tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Gambo Bakori; da Hon. Abubakar Tsanni (Soja), tare da sauran ‘yan siyasa, masu ruwa da tsaki da magoya bayan ƙungiyoyin.
Taron ya kuma jaddada muhimmancin ci gaba da tattaunawa da haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki, musamman yayin da jihar da ƙasar ke shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
