Saturday, October 17, 2026
HomeLabarai’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Toshe Hanyar Katsina Zuwa Kano

’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Toshe Hanyar Katsina Zuwa Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta ƙaryata rahotannin da ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta, waɗanda ke ikirarin cewa wasu ’Yanbindiga sun tare babbar hanyar Katsina zuwa Kano a yankin Gidan Mutum Daya, da ke Ƙaramar Hukumar Kusada ta jihar.

Rundunar ta bayyana cewa rahoton ba shi da tushe, tana mai gargadin cewa irin waɗannan bayanai na iya haifar da fargaba da ruɗani a tsakanin al’umma, musamman matafiya da masu amfani da hanyar.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ANIPR, ya fitar a ranar 16 ga Oktoba, 2026, rundunar ta bayyana cewa ainihin abin da ya faru shi ne cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kasancewa ’yan bindiga, tare da kwato dabbobi sama da 150 da ake zargin an sace.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 15 ga Oktoba, da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, lokacin da jami’an Rundunar Katsina State Community Watch Corps (KSCWC), tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai, suka kama waɗanda ake zargin a yankin Gidan Mutum Daya, bayan samun sahihan bayanan sirri.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, an bayyana sunayen waɗanda aka kama a matsayin Abdulkadir Umar, mai shekaru 23, da Suleiman Baiti, mai shekaru 21.

Bayan gudanar da tambayoyi na farko, rundunar ta ce waɗanda ake zargin sun amsa cewa suna da alaƙa da wata ƙungiyar ’yanbindiga da ke addabar wasu sassan Jihar Katsina.

Bayan haka, da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, jami’an ’yan sanda na sashen Kusada, ƙarƙashin jagorancin jami’in da ke kula da sashen (DPO), sun haɗa kai da jami’an KSCWC da ’yan sa-kai, inda suka nufi wani wuri da waɗanda ake zargin suka nuna musu.

Haka kuma, a yayin samamen, jami’an tsaron sun yi nasarar kwato dabbobi sama da 150 da ake zargin an sace, waɗanda suka haɗa da shanu, awaki da tumaki.

Rundunar ta bayyana cewa an kai dabbobin zuwa wani wuri mai tsaro domin kiyaye su, tare da ba jami’an tsaro damar ci gaba da bincike kan yadda aka sace su da kuma gano masu su.

Sanarwar ta ƙara da cewa yayin da ake jigilar dabbobin, jami’an tsaro sun dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a kan babbar hanyar Katsina zuwa Kano na ɗan lokaci.

Ta ce an ɗauki matakin ne domin ba garken dabbobin damar tsallaka hanyar cikin aminci, ba tare da jefa rayukan matafiya da sauran masu amfani da hanyar cikin haɗari ba.

Bayan an kammala tsallakar da dabbobin, jami’an tsaron sun ba da damar ci gaba da zirga-zirgar ababen hawa kamar yadda aka saba.

Rundunar ta jaddada cewa babu wani harin ’yan bindiga da aka kai a wurin, sannan babu wani rahoton da ke nuna cewa ’yan bindiga sun tare hanyar ko kuma sun yi barazana ga matafiya a lokacin da lamarin ya faru.

Ta bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, tare da tabbatar da cewa za a sanar da jama’a duk wani sabon bayani da ya samu yayin da binciken ke ci gaba.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya yaba wa jami’an tsaro da suka gudanar da aikin, bisa haɗin kai, ƙwazo da kuma gaggawar ɗaukar matakin da ya kai ga cafke waɗanda ake zargin da kwato dabbobin.

Kwamishinan ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar da matafiya cewa babbar hanyar Katsina zuwa Kano tana cikin tsaro, kuma ana iya amfani da ita ba tare da fargaba ba, bisa bayanan da rundunar ta bayar.

A ƙarshe, rundunar ’yan sandan ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da rahotannin da ba su da sahihiyar majiya, tare da guje wa yaɗa bayanan da ba a tabbatar da gaskiyarsu ba.

Ta buƙaci al’umma da su riƙa tabbatar da sahihancin duk wani labari daga majiyoyi masu inganci, musamman bayanan da suka shafi tsaro, domin kauce wa yaɗa jita-jita da ka iya tayar da hankulan jama’a ko haifar da fargaba a tsakanin matafiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments