Mawaka, ’yan fim da masu wasan barkwanci a Jihar Katsina, sun bayyana goyon bayansu ga sake zaɓen Gwamna Dikko Umar Radda da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Sun bayyana matsayarsu ne a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, 2026, yayin wani taro da aka gudanar a babban ɗakin taro na Gidauniyar Gwagware da ke kan hanyar Daura, a cikin birnin Katsina.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, a wajen taron, Mataimakin Gwamnan Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe, wanda ya wakilci Gwamna Radda, ya ƙaddamar da rabon tallafin kuɗi da mashina 13 da Mai Ba Gwamna Shawara kan Harkokin Nishadantarwa, Hon. Hassan Isah Danja, ya samar domin tallafa wa masu sana’ar nishaɗantarwa.
Da yake jawabi a madadin gwamnan, Jobe ya yaba wa masu nishadantarwa bisa gudunmawarsu wajen wayar da kan al’umma da yaɗa manufofi da ayyukan gwamnatin jihar.
Ya ce gwamnatin Radda ta mayar da hankali wajen gudanar da ayyukan raya ƙasa da inganta rayuwar al’umma a faɗin ƙananan hukumomi 34 da mazabu 361 na jihar. Ya kuma buƙaci al’ummar Katsina su fito kwansu da kwarkwatarsu domin marawa APC baya a zaɓen 2027.
Shi ma Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Katsina, Dr. Salisu Bala Zango, ya bayyana taron a matsayin wata alama ta goyon bayan da masu nishadantarwa ke bai wa gwamnatin Radda da jam’iyyar APC.
Ya yaba wa Hon. Hassan Isah Danja bisa ƙoƙarinsa na haɗa kan masu nishadantarwa da amfani da fasaharsu wajen isar da saƙonnin gwamnati ga jama’a.
A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Dikko Radda, Arch. Ahmad Musa Dangiwa, ya ce ayyukan da gwamnan ya gudanar a faɗin jihar sun ƙarfafa masa gwiwar ganin ya cancanci samun wa’adi na biyu.
Shugaban Ƙungiyar Gwagware Modern Singers, Alhaji Ibrahim Danzaki, ya kuma yaba wa gwamnan bisa tallafin da yake bai wa masu nishadantarwa, yana mai cewa mambobin ƙungiyar za su ƙara ƙaimi wajen yaɗa saƙonnin gwamnati.
Danzaki ya ce kowane ɗan ƙungiyar zai yi ƙoƙarin samar da kuri’u 20 domin tallafa wa burinsu na siyasa a zaɓe mai zuwa.
Shi ma Mai Taimakawa Gwamnan jihar Katsina kan Harakokin Nishadi da Nishadantarwa, Hon. Hassan Isah Danja, ya tabbatar wa Gwmanan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda da Bola Ahmed Tinubu, za su lashe zaben 2027 da yardar Allah.
Ya jaddada cewa, mawaka da yan fim da Masu wasan Barkwanci da sauran Masana’antar Kannywood za su tsaya tsayin daka don tabbatar da nasarar jam’iyyar APC tun daga sama har kasa.
A ƙarshen taron, mawakan gargajiya da na zamani, masu yabon Annabi (S.A.W), ’yan fim da masu wasan barkwanci sun sake jaddada goyon bayansu ga sake zaɓen Radda da Tinubu a shekarar 2027.
