Wani dattijo mai kimanin shekaru 75, wanda aka fi sani da Baba Yalo, ya auri budurwa ’yar shekara 18 a garin Yalo da ke Ƙaramar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, An ɗaura auren ne a ranar Lahadi, 8 ga Nuwamba, 2026, inda ’yan uwa da abokan arziki suka halarci bikin domin taya sabbin ma’auratan murna.
Auren ya ja hankalin al’ummar yankin tare da haifar da muhawara, musamman kan tazarar shekaru 57 da ke tsakanin ma’auratan.
Lamarin ya zama abin tattaunawa a tsakanin al’umma, inda mutane ke bayyana ra’ayoyinsu mabambanta kan auren.
