Wata yarinya mai shekara 15 a Jihar Nasarawa ta haddace Alƙur’ani Mai Girma gaba ɗaya, tare da sanin tafsirinsa.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, wannan nasara ta nuna irin ƙoƙari da jajircewar yarinyar wajen neman ilimin addinin Musulunci tun tana ƙarama.
Haddar Alƙur’ani da fahimtar tafsirinsa na daga cikin manyan nasarorin da ake ƙarfafa yara da matasa su yi ƙoƙarin cimmawa.
Lamarin ya zama abin ƙarfafa gwiwa ga iyaye da masu kula da yara wajen tallafa musu da ƙarfafa musu guiwa a fannin karatun addini da sauran ilimomi.
Mutane da dama ne suka yi fatan Allah ya ƙara mata ilimi mai amfani, Ya sanya Alƙur’ani ya zama haske da shiriya a rayuwarta, Amin.
