Wednesday, November 11, 2026
HomeLabaraiFursunoni 2 Sun Tsere Daga Gidan Yarin Okene, Duk da An Yankema...

Fursunoni 2 Sun Tsere Daga Gidan Yarin Okene, Duk da An Yankema Daya Hukunci

Hukumomin tsaro a Jihar Kogi sun fara farautar wasu fursunoni biyu da suka tsere daga gidan gyaran hali na Okene, lamarin da har yanzu ba a bayyana cikakken yadda ya faru ba.

Rahoton rundunar ’yan sandan Okene ya bayyana cewa an sanar da ita tserewar ne a ranar Lahadi, 8 ga Nuwamba, 2026, da misalin ƙarfe 10:30 na safe, bayan jami’in da ke kula da gidan yarin ya kira ’yan sanda ta waya.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, an bayyana sunayen fursunonin da suka tsere a matsayin Samson David, wanda ke zaman gidan yari bisa laifin sata, da kuma Salvation Moro, wanda aka yanke wa hukuncin fashi da makami.

Bayanan farko sun nuna cewa fursunonin sun tsere ne ta bayan katangar gidan yarin.

Rahoton ya kuma bayyana cewa an miƙa hotunan mutanen biyu ga ’yan sanda domin taimakawa wajen gano inda suke.

Bayan samun rahoton, jami’an tsaro sun fara ƙoƙarin gano su tare da mayar da su gidan yari.

Sai dai har yanzu ba a bayyana yadda suka samu damar tserewa ba, ko kuma ko an fara binciken wasu jami’an gidan yarin kan lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments