Wednesday, November 11, 2026
HomeLabaraiHisbah Za Ta Ƙara Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Da ’Yan Jarida– Shugaban Hisba...

Hisbah Za Ta Ƙara Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Da ’Yan Jarida– Shugaban Hisba a Katsina

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, Sheikh Saifiddeen Yakubu Musa, ya gana da ’yan jarida domin tattauna ayyukan hukumar da kuma ƙoƙarin da take yi na inganta aikinta a faɗin jihar.

An gudanar da taron manema labaran ne ranar Litinin 9 ga watan Nuwamba 2026, a hedikwatar hukumar da ke kan hanyar Jibiya, kusa da barikin sojoji, a birnin Katsina.

Taron ya babban Kwamandan damar bayyana nasarorin da hukumar ta samu, ƙalubalen da take fuskanta da kuma shirye-shiryenta na ƙara inganta ayyukanta.

Haka kuma, ’yan jaridar da suka halarci taron sun samu damar yi masa tambayoyi da neman ƙarin bayani kan ayyuka da nauyin da ke rataye a wuyan hukumar, da kuma tsare-tsarenta na gaba.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Ganawar ta mayar da hankali kan muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumar da kafafen yaɗa labarai wajen wayar da kan al’umma da sanar da jama’a ayyukan da Hisbah ke gudanarwa a jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments