Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Sunusi Sabi’u Zakariyya, bisa zargin ɗaura wa kansa aure da wata budurwa mai suna Zainab, wadda ta gudu daga Jihar Kebbi zuwa Kano saboda ƙaurace wa auren dole.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Kwamandan Hisbah na Ƙaramar Hukumar Birni, Hamidan Tanko Alasaka, ne ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan binciken da hukumar ke gudanarwa.
A cewar Zainab, ta bar Birnin Kebbi ne bayan mahaifinta ya nuna niyyar aurar da ita ba tare da yardarta ba. Ta ce ta haɗu da Sunusi ne ta hanyar waya, daga bisani ta koma Kano inda ta zauna a gidan yayarsa na tsawon watanni biyu.
Shi kuwa Sunusi, wanda tuni yake da matar aure, ya bayyana cewa ya nemi wasu mutane tare da wani abokinsa domin su taka rawar waliyyai wajen ɗaura auren nasu, inda aka amince da sadakin Naira 70,000.
Kwamandan Hisbah ya ce mazauna unguwar ne suka kai rahoton lamarin ga hukumar, bayan zargin cewa an gudanar da ɗaurin auren ba bisa ƙa’ida ba a wani shago.
Ya ƙara da cewa hukumar ta kama waɗanda abin ya shafa, kuma tana ci gaba da bincike kafin miƙa su zuwa hedikwatar Hisbah domin ɗaukar matakin da ya dace.
