Thursday, November 12, 2026
HomeLabaraiDoka Za Ta Yi Aiki Ga Duk Waɗanda Suka Kawo Ma Taron...

Doka Za Ta Yi Aiki Ga Duk Waɗanda Suka Kawo Ma Taron APC Hari a Shiyyar Funtua– Dangiwa

Shugaban Yakin Neman Zaben Tinubu da Dikko a 2027 na jihar Katsina, Arch Ahmed Musa Dangiwa, ya ce duk Mutanen da aka tura domin su tarwatsa ma su taro Yakin Neman Zabensu a Wasu yankunan Shiyyar Funtua, tabbas su sani za su dauki mataki a kansu ko ‘Ya’yan waye.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci taron Manema Labarai cikin hedikwatar ofishin yaƙin neman zaɓen Jam’iyyar APC a jihar Katsina, ranar Alhamis 12 ga watan Nuwamba 2026.

Tunda farko, Dangiwa ya ce da sun biyewa waɗanda suka kawo harin da an rasa rayuka da dama, amma saboda muhimmancin Dan Adam suka riƙa hana matasan da suke a bangaren APC su tarbi waɗanda suka kawo harin.

Ya kara da cewa, amma daga cikin Kananan Hukumomi 11 na Shiyyar Funtua duk sun Kammala Yakin Neman Zaben su lafiya ba tare da wata tangarda ba, inda ya ce sai da sukai Kwanaki 11 a yankunan kuma ya tabbatar da cewa al’umma za su sake zaben jam’iyyar APC karo na biyu.

Kazalika, ya sanar da cewa, cikin Yan kwanakin nan za su shiga Shiyyar Daura domin neman kurin jama’a domin sake zaben jam’iyyar APC tun daga kasa har sama.

Haka kuma, ya godewa ‘Yanjarida duba da irin gudummuwar da suke ba su wajen yada manufofin su, tare da sauran magoya bayan jam’iyyar daga sassa daban-daban na jihar Katsina.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments