Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama wasu makamai masu yawa da ake zargin ana safarar su daga Jamhuriyar Nijar zuwa hannun ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Rahoton ya nuna cewa jami’an DSS sun kama makaman ne a ranar Talata, 10 ga Nuwamba, a garin Dawakawa da ke ƙaramar hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto.
Kayayyakin da aka kwato sun haɗa da bindigogin AK-47 guda 21, manyan bindigogin PKT guda huɗu da kuma magazin guda 825.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda ake zargin sun yi amfani da raƙuma wajen safarar makaman ta kan iyakar Najeriya da Nijar, domin kauce wa jami’an tsaro.
Ana zargin an shirya kai makaman ne ga ’yan bindiga da ke gudanar da ayyukansu a yankin Arewa maso Yammacin ƙasar.
