Thursday, November 12, 2026
HomeLabaraiKanwan Katsina Ya Gargaɗi ’Yan Jarida Kan Bin Ƙa’idojin Aiki

Kanwan Katsina Ya Gargaɗi ’Yan Jarida Kan Bin Ƙa’idojin Aiki

Kanwan Katsina, kuma Hakimin Ketare, Alhaji Usman Bello Kankara, mni, ya buƙaci masu gudanar da kafafen yaɗa labarai na intanet a Jihar Katsina da su riƙa gudanar da ayyukansu bisa ƙa’idoji da dokokin aikin jarida domin tabbatar da sahihanci da amincewar al’umma.

Basaraken ya yi wannan gargaɗi ne yayin bikin rantsar da shugabannin sabuwar ƙungiyar masu aikin jarida ta kafafen intanet (Online Media Chapel) ta Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), reshen Jihar Katsina.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Alhaji Usman Bello Kankara, wanda shi ne Uban Ƙungiyar NUJ ta Jihar Katsina, ya jaddada cewa, bin ƙa’idojin aikin jarida wajibi ne ga duk wanda ke gudanar da harkokin yaɗa labarai, ba tare da la’akari da kafar da yake amfani da ita ba.

Ya ce ya kamata masu aikin jarida su kasance masu ƙwarewa, gaskiya, adalci da ɗaukar nauyin dukkan bayanan da suke yaɗawa, yana mai cewa waɗannan halaye ne ke gina amincewar jama’a tare da ɗaukaka martabar kafafen yaɗa labarai.

Basaraken ya kuma buƙaci ’yan ƙungiyar da su riƙa tantance sahihancin bayanan da suka samu kafin wallafa su, domin kauce wa yaɗa labaran ƙarya da bayanan da ka iya haifar da ruɗani ko rashin fahimta a tsakanin al’umma.

Haka kuma, ya shawarci sabbin shugabannin ƙungiyar da su samar da ingantaccen tsarin gudanarwa, haɗin kai da fahimtar juna tsakanin mambobi, tare da tabbatar da cewa kowane ɗan ƙungiya yana sauke nauyin da ke kansa.

Kanwan Katsina ya kuma jaddada muhimmancin biyan kuɗaɗen ƙungiya a kan lokaci, yana mai buƙatar shugabannin su kafa ofishin sakatariya domin sauƙaƙa gudanar da ayyukan ƙungiyar da inganta hulɗa tsakanin mambobinta.

A yayin taron, an rantsar da shugabannin ƙungiyar waɗanda za su jagorance ta na tsawon shekara guda, inda Abubakar Shafi’i na Mobile Media ya zama shugaban farko.

Sauran waɗanda aka rantsar sun haɗa da Mustapha Sadiq na Katsina Post a matsayin sakatare, yayin da Zaharadeen Ishaq na Katsina Times ya zama ma’aji.

Alhaji Kankara ya bayyana cewa, a matsayinsa na Uban Ƙungiyar NUJ a jihar, a shirye yake a kodayaushe ya ba sabbin shugabannin goyon baya, shawarwari da jagoranci domin samun nasarar ayyukan ƙungiyar.

Ya kuma yi musu fatan alheri tare da buƙatar su yi amfani da damar da aka ba su wajen samar da shugabanci nagari da kuma kare martabar aikin jarida.

Rantsar da shugabannin na zuwa ne a wani mataki na ƙarfafa tsarin aikin jarida na kafafen intanet a Jihar Katsina, musamman wajen haɗa masu gudanar da kafafen da samar da tsari da zai inganta ƙwarewa, bin dokokin sana’a da yaɗa sahihan bayanai ga al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments