Rikici tsakanin makiyaya da manoma ya ɓarke a ƙauyen Turawa da ke Ƙaramar Hukumar Sule Tankarkar a Jihar Jigawa, inda mutum ɗaya mai shekaru 45 ya jikkata.
Rundunar Tsaron Fararen Hula ta Ƙasa (NSCDC) ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan zargin lalata amfanin gona da aka yi wa wasu makiyaya, lamarin da ya haifar da arangama tsakaninsu da manoma.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Wanda ya jikkata mai suna Babangida Danjuma, an harbe shi da kibiya, inda aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Rasheed Shekoni da ke Dutse domin samun kulawar likitoci.
Rundunar ta ce makiyayan sun tsere daga wurin, inda suka bar jakuna shida da saniya ɗaya.
A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da sa ido a yankin domin hana sake barkewar rikici.
