Sarkin Rano, Ambasada Dakta Muhammad Isa Umar, ya yi kira ga al’ummar Masarautar Rano da ke Jihar Kano da su zaɓi shugabanni bisa cancanta da nagarta a babban zaɓen 2027, tare da guje wa sayar da ƙuri’unsu.
Ya yi wannan kiran ne yayin wani taron wayar da kan jama’a da Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA), reshen Jihar Kano, ta shirya a Masarautar Rano.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Sakataren Yaɗa Labaran Masarautar, Nasiru Habu Faragai, ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba, 2026.
Sanarwar ta ce Sarkin ya buƙaci hakimai, dagatai, limamai da sauran shugabannin gargajiya da su wayar da kan al’umma kan muhimmancin mallakar katin zaɓe da shiga harkokin zaɓe.
Ya kuma jaddada buƙatar gudanar da zaɓe cikin lumana, tare da kira ga jama’a da kada su bari a sayi ƙuri’unsu, domin zaɓe haƙƙi ne da ya kamata kowa ya yi amfani da shi cikin gaskiya da sanin ya kamata.
A nasa jawabin, Daraktan NOA na Jihar Kano, Malam Nura Liman, ya bayyana manufar shirya taron wayar da kan jama’a.
