Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi wasu ’yan siyasa, musamman gwamnonin jihohi, da tsangwamar mutanen da ke hulɗa da shi saboda siyasa.
Atiku ya yi zargin cewa an dakatar da wani limami daga aikinsa bayan ya jagorance shi sallar jam’i a wani masallaci da ya halarta.
Ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin ziyarar girmamawa da ya kai ga Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu, a yayin rangadin siyasarsa a jihar.
Atiku ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed bisa ba shi damar ziyartar masarautar, yana mai cewa a wasu jihohin ana hana shi ganawa da sarakunan gargajiya.
Ya ce dakatar da limamin ya nuna yadda wasu gwamnonin ke tauye ikon sarakunan gargajiya da kuma yin katsalandan a harkokin da suka shafe su.
“Abin takaici ne yadda abin ya kai ga dakatar da limamin masallacin da na yi sallah a cikinsa saboda ya jagorance mu sallah,” in ji Atiku.
Ya ƙara da cewa a tarihin Arewacin Najeriya, limamai suna ƙarƙashin ikon sarakunan gargajiya, musamman masu sarauta mafi girma, ba gwamnonin jihohi ba.
Atiku ya kuma bayyana muhimmancin masarautun gargajiya, yana mai cewa su ne tushen al’adu da tarihin al’umma, kuma ya kamata a mutunta matsayinsu.
Ya yi addu’ar Allah ya ba shi damar yin abin da ya dace idan ya samu dama ta jagorantar ƙasar.
