Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta haramta fitar da gyaɗa zuwa ƙasashen waje, domin tabbatar da wadatar amfanin gonar a kasuwannin cikin gida da kuma tallafa wa masana’antun sarrafa gyaɗa na ƙasar.
Ministan Kasuwanci da Masana’antu, Abdoulaye Seydou, ne ya sanar da matakin a ranar Juma’a yayin taron manema labarai a Yamai, babban birnin ƙasar.
Matakin, wanda aka tabbatar da shi ta wata doka mai kwanan wata 11 ga Nuwamba, 2026, na da manufar kare masu sayen gyaɗa a cikin gida da samar da isasshen kayan amfanin gona ga masana’antun sarrafawa.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, sai dai gwamnatin ta ce za ta iya bayar da izinin fitar da gyaɗa zuwa ƙasashen ƙungiyar AES a wasu yanayi na musamman, bisa ƙa’idojin da aka tsara.
Ministan ya gargaɗi cewa za a ƙwace duk wata gyaɗa da aka yi ƙoƙarin fitarwa ba tare da izini ba, inda jami’an kwastam da jami’an tsaro za su tabbatar da aiwatar da dokar.
Haka kuma, gwamnatin ta buƙaci ma’aikatun gwamnati, jami’o’i, barikokin sojoji da sauran cibiyoyin gwamnati da su fifita sayen kayayyakin da ake ƙerawa a cikin gida.
Matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Nijar na ƙarfafa tattalin arziƙin ƙasa ta hanyar bunƙasa noma da sarrafa amfanin gona a cikin gida.
