Monday, November 16, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Dikko Za Ta Sake Gina Ƙofofin da Aka Rushe a Birnin...

Gwamnatin Dikko Za Ta Sake Gina Ƙofofin da Aka Rushe a Birnin Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana shirin sake gina tsofaffin ƙofofin Birnin Katsina da aka rushe sakamakon ayyukan Shirin Sabunta Birane (Urban Renewal Programme) da gwamnatin Gwamna Dikko Umar Radda ke aiwatarwa.

Gwamnatin ta ce Gwamna Radda ya bayar da umarnin fara dukkan shirye-shiryen da suka dace domin sake gina ƙofofin birnin, waɗanda aka rushe yayin gudanar da ayyukan sabunta birnin Katsina.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da Kwamitin Aiwatarwa kan Rahoton Kwamitin Jiha na Maido da Martabar Wuraren Tarihi na Jihar Katsina ya fitar, mai ɗauke da kwanan wata 9 ga Nuwamba, 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin jihar na bai wa abubuwan tarihi da al’adun gargajiya muhimmanci, dalilin da ya sa gwamnan ya kafa kwamitin musamman domin kula da harkokin dawo da martabar wuraren tarihi da kare al’adun gargajiyar jihar.

Da yake magana a madadin shugaban kwamitin, Dakta Mustapha Shehu, mataimakinsa, Dakta Sada Salisu Rumah, ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa tuni mambobin kwamitin suka fara aiki kan batun sake gina ƙofofin birnin.

Ya ce kwamitin ya samu buƙatu da dama daga al’umma, inda mutane suka nuna damuwarsu tare da neman a sake gina ƙofofin da aka rushe.

Dakta Rumah ya ƙara da cewa Gwamna Radda ya yaba da yadda al’umma suka nuna damuwa kan lamarin, tare da tabbatar musu da cewa gwamnatinsa ba za ta bari a kawar da wani muhimmin wurin tarihi na jihar ba.

Ya jaddada cewa gwamnatin jihar na da aniyar kare martabar wuraren tarihi da al’adun gargajiyar Katsina domin amfanin al’umma da kuma al’ummomi masu zuwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments