Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta bayyana cewa dakarun sojin ƙasar sun kuɓutar da mutane 125 da aka yi garkuwa da su, sun hallaka ’yan ta’adda takwas tare da kama mutum 10 da ake zargi da taimaka wa ƙungiyoyin ta’addanci a sassa daban-daban na ƙasar.
Sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaron, Manjo Janar Michael Onoja, ya fitar, ta ce an gudanar da ayyukan ne tsakanin 6 zuwa 12 ga Nuwamba, 2026. Haka kuma, ’yan ta’adda 12 tare da wasu iyalansu sun miƙa wuya.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Daga cikin mutanen da aka kuɓutar akwai matafiya 119 da aka yi garkuwa da su a ranar 6 ga Nuwamba a kan hanyar Dutsen Kura–Bulazarma–Kamuya, kusa da Buratai, a Ƙaramar Hukumar Biu ta Jihar Borno.
Sanarwar ta ce sojoji sun bi sawun maharan ta yankin Mangari zuwa Dora, lamarin da ya tilasta musu sakin mutanen.
Mutanen da aka kuɓutar sun haɗa da maza 69, mata 35 da yara 15. Sai dai an gano gawar direban motar da aka yi garkuwa da shi tare da sauran matafiyan.
A Jihar Zamfara kuwa, sojojin sun kuɓutar da wasu mutane biyar a samame daban-daban, yayin da wasu mutum uku suka samu ’yanci bayan harin da aka kai wa matafiya a hanyar Kombo zuwa Gurusu, Ƙaramar Hukumar Bukkuyum.
Haka kuma, dakarun sun gudanar da ayyuka a jihohin Bauchi, Filato, Taraba, Benuwai, Nasarawa, Neja, Kwara da Oyo, inda suka ƙwato makamai da alburusai tare da rusa wasu sansanonin ’yan bindiga.
A Jihar Neja, sojojin da ke aikin tsaro a yankin Gandun Dajin Kainji sun tarwatsa bama-bamai guda biyar da aka ƙera a gida, sun dakile hare-hare biyu tare da kashe wasu mutum biyu da ake zargin ’yan ta’adda ne.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar garkuwa da mutane da hare-haren ’yan bindiga ke ci gaba da zama babban ƙalubalen tsaro a sassan Nijeriya.
