Kwalejin Shari’a ta Legal Ta Haramta Shiga Jarabawa Da Niƙabi da Wayar Hannu a Kano
Kwalejin Nazarin Addinin Musulunci da Shari’a ta Legal da ke Kano ta haramta wa ɗalibanta shiga ɗakin jarabawa sanye da niƙabi ko abin rufe fuska, yayin da take shirin fara jarabawar zangon karatu na farko.
Sanarwar da Shugaban Kwalejin, Dr. Ali Tamasi Mu’az, ya fitar ta ce dokar za ta fara aiki ne gabanin jarabawar da aka tsara farawa ranar Litinin, 16 ga Nuwamba, 2026.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Baya ga niƙabi, kwalejin ta haramta shiga ɗakin jarabawa da wayar hannu, na’urar sauraron sauti, baƙin gilashi, littattafai ko wasu takardun da ke da alaƙa da darasin da ake jarabawa.
Haka kuma, an haramta wa ɗalibai shiga ɗakin jarabawa tare da ƙananan yara.
Shugaban kwalejin ya buƙaci ɗaliban Pre-Diploma, Diploma, Advanced Diploma da NCE, na karatun cikakken lokaci da na wucin gadi, su riƙa zuwa ɗakin jarabawa aƙalla minti 15 kafin lokacin farawa, tare da katin shaidar jarabawarsu.
Ya kuma yi gargaɗin cewa ɗalibin da aka samu da satar amsa, yin jarabawa a madadin wani ko karya dokokin jarabawa zai fuskanci hukuncin ladabtarwa.
Hukuncin na iya haɗawa da gargaɗi, dakatarwa, kora daga kwalejin ko gurfanarwa a gaban kotu.
