Tuesday, November 17, 2026
HomeLabarai'Yar Shekara 16 Ta Sayar Da Jaririyarta Kan Naira Miliyan 2 a...

‘Yar Shekara 16 Ta Sayar Da Jaririyarta Kan Naira Miliyan 2 a Legas

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta ceto wata jaririyar da aka haifa kwana guda tare da kama mutum huɗu, ciki har da mahaifiyarta mai shekaru 16, bisa zargin sayar da jaririn kan kuɗi har naira miliyan biyu a Jihar Legas.

Jaridar Punch ta rawaito cewa yarinyar mai suna Funmilayo Sanwo-Olu ta amsa cewa ta sayar da jaririyar ne saboda matsin tattalin arziki da matsalolin kuɗi da take fuskanta.

Lamarin ya bankado ne bayan wata mata ta kai ƙorafi ga ’yan sanda kan wani mai haya a gidanta, mai suna Favour Ipoko, mai shekaru 47, wadda ta sanar da ita cewa kada ta yi mamaki idan ta ji kukan jariri a gidanta, duk da cewa ba ta san tana da ciki ba.

Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda sun gudanar da bincike tare da cafke Favour da mijinta, Isaac Ipoko, mai shekaru 30, inda suka gano jaririyar mai kwana ɗaya da haihuwa.

Binciken da jami’an suka zurfafa ya kai ga cafke wata mata mai suna Chantel Armstrong, mai shekaru 46, wadda ake zargin ta taka rawa wajen hada-hadar sayar da jaririyar, da kuma mahaifiyar jaririn.

Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Ani Iniedu, ne ya bayyana hakan cikin rahoton ayyukan rundunar da aka fitar a ƙarshen makon da ya gabata.

Ya ce an ceto jaririyar cikin ƙoshin lafiya, yayin da aka miƙa waɗanda ake zargin zuwa hannun jami’an sashen binciken manyan laifuka na jihar, SCID, da ke Panti, domin zurfafa bincike.

Wannan lamari na zuwa ne bayan wani samame da jami’an hukumar NSCDC suka gudanar a watan Afrilu a wani gida da ake zargin ana gudanar da sana’ar sayar da jarirai a Okuju, Ilado, yankin Badagry na Jihar Legas.

A yayin samamen, jami’an sun ceto mata 18 masu juna biyu da yara 10, tare da kama wasu mutane biyu da ake zargin su ne masu gudanar da wurin, Joy Okeke da Raphael Agwu.

Bincike ya nuna cewa an yaudari matan ne ta hanyar tallan da aka yi a Facebook, inda aka yi musu alƙawarin kuɗi tsakanin naira 500,000 da miliyan 1.8 bayan haihuwar jariransu.

Lamarin ya sake jawo hankalin jama’a kan yadda ake cin zarafin mata masu rauni da kuma safarar jarirai ta hanyar haramtattun hanyoyi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments