Saturday, November 21, 2026
HomeLabaraiKotu Ta Umarci Tsare Matashi Kan Zargin Hallaka Wani a Kano

Kotu Ta Umarci Tsare Matashi Kan Zargin Hallaka Wani a Kano

Wata Kotun Majistare mai lamba 27 da ke Kano ta bayar da umarnin tsare wani matashi mai suna Musa Umar a gidan gyaran hali, bisa zargin haɗa baki wajen kashe Saminu Haruna.

Mai Shari’a Hauwa Abba Musa ce ta bayar da umarnin bayan gurfanar da matashin a gaban kotun kan tuhume-tuhumen haɗa baki wajen aikata laifi da kuma kisan kai.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Lauyar gwamnati, Barrister Maryam Halilu Dantiye, ce ta gabatar da takardar tuhumar a gaban kotun.

Bayan karanta tuhume-tuhumen, kotun ta bayar da umarnin ci gaba da tsare wanda ake zargin har sai gwamnati ta bayar da shawarar shari’a kan lamarin.

Ana zargin Musa Umar da wani mutum da ya tsere da daba wa marigayi Saminu Haruna wuƙa har ya mutu, bayan wani saɓani da ya shiga tsakaninsu a unguwar Rijiyar Lemo da ke Kano.

Kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 7 ga Janairu, 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments