Friday, November 20, 2026
HomeLabaraiEFCC Ta Gurfanar da Wani Mutum Kan Zargin Damfarar Miliyan 7.8 Na...

EFCC Ta Gurfanar da Wani Mutum Kan Zargin Damfarar Miliyan 7.8 Na Filaye a Jos

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta gurfanar da wani mutum mai suna Sani Umar Ahmad bisa zargin damfarar wani mutum, Umar Abdullahi, kuɗi Naira miliyan 7.85 da sunan zuba jari a harkar filaye a Abuja.

An gurfanar da Ahmad ne a ranar 19 ga Nuwamba, 2026, a gaban Mai Shari’a Dorcas V. Agishi ta Babbar Kotun Tarayya da ke Jos, Jihar Filato, bisa tuhume-tuhume guda biyu na karɓar kuɗi ta hanyar yaudara.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, EFCC ta zargi wanda ake tuhuma da haɗa baki da Nasiru Umar Labaran, wanda har yanzu yake tsere, wajen karɓar kuɗin daga hannun Umar Abdullahi ta asusun bankunansu guda biyu da ke Taj Bank da First Bank.

Hukumar ta bayyana cewa, tsakanin watan Mayu zuwa Yunin 2025, Ahmad ya karɓi Naira miliyan 7.85 bisa zargin cewa kuɗin za a yi amfani da su wajen sayen filaye a Abuja waɗanda ake ikirarin na ubangidansa, Nasiru Umar Labaran ne.

Sai dai wanda ake tuhuma ya musanta aikata laifukan bayan an karanta masa tuhume-tuhumen a kotu.

Lauyan EFCC, M. D. Aliyu, ya nemi kotun ta sanya ranar fara shari’a tare da bayar da umarnin tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali.

Sai dai lauyan wanda ake tuhuma, P. N. Washpam, ya shigar da buƙatar belinsa, inda ya roƙi kotun ta yi amfani da ikonta wajen amincewa da buƙatar.

Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Mai Shari’a Agishi ta ɗage shari’ar zuwa ranar 3 ga Disamba, 2026, domin sauraron buƙatar beli, tare da bayar da umarnin ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali na Jos.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments