Babbar Kotun Jihar Adamawa da ke zamanta a Yola, ta yanke wa wani mutum mai suna Shuaibu Usman hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 10 ba tare da zabin biyan tara ba, bisa samunsa da laifin damfara.
Mai shari’a Benjamin Manji ne ya yanke hukuncin a ranar 17 ga Nuwamba, 2026, bayan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, reshen Gombe, ta gurfanar da shi bisa zargin damfarar Hamza Abba Ishaka.
A cewar tuhumar, Usman ya yaudari Ishaka a watan Satumban 2022, inda ya karɓi kuɗin da yawansu ya kai Naira miliyan 7,483,950, bisa hujjar cewa zai saka su a harkar kasuwancin haƙar kuɗaɗen dijital (Digital Mining).
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Sai dai harkar ta zama yaudara, inda wanda aka damfara ya ce duk ƙoƙarin da ya yi na ganin an mayar masa da kuɗinsa ya ci tura.
An gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu a ranar 17 ga Fabrairun 2025, inda ya musanta aikata laifin, lamarin da ya kai ga fara shari’a.
A yayin shari’ar, lauyan masu gabatar da ƙara, AM Labaran, ya gabatar da shaidu biyu da wasu hujjoji, yayin da lauyan wanda ake ƙara, AY Mohammed, ya gabatar da shaidu huɗu da hujjoji huɗu domin kare wanda yake wakilta.
Bayan sauraron dukkan ɓangarorin, kotun ta same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari ba tare da zabin tara ba.
Haka kuma, kotun ta umarci wanda aka yanke wa hukuncin da ya mayar wa Hamza Ishaka dukkan kuɗin da ya karɓa, wato Naira 7,483,950.
Rahoton EFCC ya bayyana cewa, lamarin ya fara ne bayan hukumar ta samu ƙorafi daga Hamza Ishaka, wanda ya zargi Shuaibu Usman da damfararsa ta hanyar amfani da sunan kasuwancin Digital Mining.
