Wata mata mai shekaru 70 ta tsira da rai bayan da ta faɗa cikin wata rijiya mai zurfin ƙafa 60 a unguwar Oworonshoki, da ke ƙaramar hukumar Kosofe a Jihar Legas.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Lamarin ya faru ne a unguwar Abiola Street, mai lamba 37, inda jami’an hukumar kashe gobara da ceto ta Jihar Legas suka kai ɗauki da sanyin safiyar Lahadi, bayan samun kiran neman agaji.
Jami’an hukumar sun yi nasarar ceto matar daga cikin rijiyar tana da rai, lamarin da ya sanya iyalanta cikin farin ciki bayan fargabar da suka shiga.
Babbar jami’ar hukumar kashe gobara da ceto ta Jihar Legas, Margaret Adeseye, ce ta tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi.
Adeseye ta bayyana cewa bayan ceto matar, jami’an sun duba lafiyarta, inda suka tabbatar da cewa yanayinta ya daidaita kafin daga bisani su miƙa ta ga iyalanta.
Sai dai har yanzu ba a bayyana musabbabin faɗawar matar cikin rijiyar ba.
