Monday, November 23, 2026
HomeLabaraiGumi Ya Roki a Sauke Duk Sarkin da Aka Samu da Laifin...

Gumi Ya Roki a Sauke Duk Sarkin da Aka Samu da Laifin Badala a Najeriy

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi kira da a sauke duk wani sarki da aka tabbatar da aikata laifin lalata, domin kare martabar sarakuna da mutuncin masarautun gargajiya.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Gumin ya bayyana hakan ne bayan bullar zargin cin zarafin wata mata ‘yar yawon buɗe ido da ake yi wa Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk.

Matar, wadda ke amfani da shafin Instagram mai suna @beduinqa, ta yi zargin cewa sarkin ya taɓa ƙirjinta ba tare da izininta ba, lokacin da ta kai masa ziyara a fadarsa ranar 14 ga Nuwamba, 2026.

A cewar matar, ta nuna rashin jin daɗinta kan abin da ta ce ya faru, amma ta zargi sarkin da mayar da martani ta hanyar dariya.

Ta kuma bayyana cewa ta yi amfani da tabarau mai ɗaukar bidiyo wajen nadar abin da ya faru, sai dai ta ce ta jira har ta kammala rangadin da take yi a Najeriya ta fice daga ƙasar kafin ta bayyana zargin.

A nasa martanin, Sheikh Gumi ya ce duk wani sarki da aka tabbatar da aikata irin wannan laifi ya kamata a sauke shi daga sarautarsa nan take, tare da naɗa wanda zai maye gurbinsa.

Haka kuma, ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta buƙaci rundunar ‘yan sandan Najeriya da gwamnatin jihar Katsina su gudanar da bincike kan zargin da matar ta gabatar.

Sai dai har yanzu zargin bai zama tabbataccen laifi ba, don haka ana buƙatar gudanar da bincike mai zaman kansa, tare da bai wa dukkan ɓangarorin da abin ya shafa damar bayyana matsayinsu domin gano gaskiyar lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments