Aƙalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu biyar suka jikkata sakamakon wani rikici tsakanin manoma da makiyaya a garin Wumtal da ke Ƙaramar Hukumar Song ta Jihar Adamawa.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya ɓarke ne ranar Lahadi, bayan da wani makiyayi ya yi zargin shiga gonar wani manomi tare da yin ɓarna a cikinta, lamarin da ya haifar da saɓani tsakanin ɓangarorin biyu.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Kansilan da ke wakiltar mazaɓar Gudu/Mboi, Danladi Yakubu, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce mutane biyu sun mutu, yayin da wasu biyar suka samu raunuka.
Haka kuma, rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta tabbatar da faruwar rikicin ta bakin kakakinta, CSP Suleiman Nguroje.
Ya bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke wasu mutane da ake zargi da hannu a rikicin, inda suka fara gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin da kuma tabbatar da cewa waɗanda ke da hannu sun fuskanci hukunci bisa tanadin doka.
Nguroje ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun samu nasarar shawo kan lamarin, inda aka dawo da zaman lafiya a yankin.
Rikicin manoma da makiyaya na ci gaba da zama ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen tsaro a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda ake samun asarar rayuka da dukiyoyi sakamakon saɓani kan filayen noma, wuraren kiwo da hanyoyin wucewar dabbobi.
