Saturday, November 28, 2026
HomeLabaraiKwankwaso Ya Zargi Abba da Neman EFCC ta Bincike Shi

Kwankwaso Ya Zargi Abba da Neman EFCC ta Bincike Shi

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da neman hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta bincike shi.

Kwankwaso ya yi zargin cewa gwamnan ya miƙa takardar buƙata ga hukumar watanni da suka gabata domin ta bincike shi, amma EFCC ta ƙi amincewa da buƙatar.

A cikin wata sanarwa, tsohon gwamnan ya ce bayan yunƙurin ya ci tura, sai aka yi amfani da wata ƙungiya mai suna Society for Anti-Corruption and Good Governance Initiative (SACGGI) wajen shirya zanga-zanga a ofishin EFCC domin matsa mata lamba.

Ya kuma zargi Abba da wasu daga cikin jami’an gwamnatinsa da amfani da kafafen yaɗa labarai wajen yaɗa bayanan da ke ƙoƙarin ɓata masa suna.

Kwankwaso ya ce waɗannan matakai na da alaƙa da siyasar zaɓen 2027, yana mai zargin cewa ana ƙoƙarin raunana shi da sauran ‘yan takarar tafiyarsa.

Ya kuma zargi gwamnan da ƙoƙarin amfani da hukumomi domin hana ɗan takararsu na gwamna, Aminu Abdussalam, shiga zaɓen 2027.

Sai dai Kwankwaso ya yabawa EFCC bisa yadda ya ce ta gudanar da gayyatar da ta taɓa yi masa sau biyu a lokacin da yake riƙe da muƙaman gwamnati.

Ya buƙaci ‘yan siyasa da su mutunta ‘yancin hukumomin gwamnati, tare da guje wa amfani da su wajen cimma muradun siyasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments