Akalla mutane 40, ciki har da manoma, makiyaya, mata, yara da jami’an tsaro, sun mutu sakamakon hare-hare da suka ƙaru a sassan Jihar Filato cikin makonni uku.
Hare-haren sun kuma jikkata wasu, tare da ƙona gidaje da kashe ko satar shanu a ƙananan hukumomi da dama, ciki har da Bassa, Barkin Ladi, Riyom, Mangu, Bokkos da Qua’an Pan.
A sabon harin da aka kai ƙauyen Tafi Gana da ke ƙaramar hukumar Bassa, ’yan sanda sun ce an kashe mutane 17, yayin da ƙungiyar Irigwe Development Association ta ce adadin ya kai 19, bayan wasu uku sun rasu a asibiti. Haka kuma, wasu huɗu sun jikkata.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, a gefe guda, ƙungiyar Fulani ta Coalition of Fulani Registered Organisations ta roƙi Shugaba Bola Tinubu da ya binciki kashe-kashe, satar shanu da lalata dukiyoyin Fulani, tana zargin an kashe ko jikkata mutane 95, tare da sace ko kashe shanu kusan 1,240 tsakanin Afrilu da Nuwamba.
Ƙungiyar Irigwe ta zargi makiyaya da hannu a sabon harin, amma MACBAN ta ƙaryata zargin, tana kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa domin kauce wa zargin da zai ƙara rura wutar rikici.
Gwamnatin Filato da ’yan sanda sun yi Allah-wadai da hare-haren, tare da tabbatar da ƙara tsaurara matakan tsaro da fara bincike domin gano waɗanda suka aikata laifukan.
Hare-haren na ci gaba duk da alƙawarin Shugaba Tinubu na kawo ƙarshen rikicin da ya yi lokacin ziyararsa jihar watanni bakwai da suka gabata.
