Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi kakkausar suka kan harin kunar bakin wake da ya auku a masallacin kasuwar Gamboru da ke Maiduguri, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu 35.
Rahotanni sun nuna cewa ɗan kunar bakin waken ne ya kutsa kai cikin masallacin a daidai lokacin da masu ibada ke gudanar da sallar Magariba a daren Laraba, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici da jimami.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da ya fitar, Gwamna Zulum ya bayyana harin a matsayin mummunan aiki da ke nuna rashin mutunta addini da darajar rayuwar ɗan Adam, yana mai cewa kai hari a wurin ibada “cin zarafi ne ga darajar masallaci a lokacin da bayin Allah ke ibada”.
Gwamnan ya bukaci al’umma da hukumomin tsaro da su ƙara sa ido tare da ɗaukar matakan tsaro masu tsauri, musamman a wuraren ibada da kasuwanni, duba da lokacin bukukuwan da ake ciki.
Haka kuma, Zulum ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, yana addu’ar Allah ya jikansu da rahama, tare da fatan samun sauƙin warkewa ga waɗanda suka jikkata.
Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakan da suka dace domin hana sake aukuwar irin wannan hari a lokacin bukukuwa da ma bayan haka, yana mai jaddada kudurin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Borno.
