Rundunar ƴansandan Nijeriya ta kama wasu mutane biyu da ake zargi ‘yan fashin daji ne da garkuwa da mutane a jihohin Katsina, Zamfara, Neja da Kwara.
An kama su ne a ranar 19 ga Disamba a yankin Komen–Masallaci da ke karamar hukumar Kaiama ta jihar Kwara.
Daya daga cikin wadanda aka kama, Abubakar Usman (Siddi), shi ne wanda aka gani a bidiyon da ya yadu yana nuna makamai da kudi, yayin da na biyun shi ne Shehu Mohammadu (Gide).
Jami’an tsaro sun kwato babur Honda Ace 125, kudi N500,000 da bindigar AK-47 tare da harsashi 20.
Ƴansanda sun ce bincike ya nuna cewa su mambobi ne na wata kungiyar ‘yan fashin daji da ke addabar jihohi da dama, kuma suna hada-hadar samar da makamai.
Rundunar ta ce wadanda ake zargin suna bada hadin kai ga masu bincike, tare da bukatar jama’a su rika bayar da sahihan bayanai domin taimakawa ayyukan tsaro.
