Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party (LP), Peter Obi, na dab da shiga jam’iyyar ADC, gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Wata majiya a jam’iyyar ta shaida cewa Obi ya kammala shirye-shiryen shiga ADC tare da gudanar da taron bayyana matsayinsa a Enugu ranar 31 ga Disamba, yayin da magoya bayansa suka fara shirye-shiryen sauya sheƙa.
Jaridar The Punch ta rawaito cewa ya kuma gana da Shugaban ADC na ƙasa, David Mark, domin sabunta goyon baya ga haɗakar jam’iyyar.
Sai dai Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce babu sanarwa a hukumance tukuna, duk da cewa tattaunawa na gudana. Haka kuma, Obidient Movement ta ce Obi ne kaɗai zai iya yin bayani kan lamarin.
A halin da ake ciki, ADC ta sanar da shirin gudanar da taron ƙasa a tsakiyar 2026 domin sake tsara jam’iyyar da kuma fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027. Jam’iyyar ta ce za ta mayar da hankali kan faɗaɗa membobinta da ƙarfafa tsarinta a faɗin ƙasa, tare da shirya taruka biyu a 2026—na amincewa da shawarwarin NEC da kuma zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa.
