HomeSashen Hausa'Yanta'adda Sun Kai Hari Ayarin 'Yan Ɗaurin Aure, Sun Sace Amarya a...

‘Yanta’adda Sun Kai Hari Ayarin ‘Yan Ɗaurin Aure, Sun Sace Amarya a Jihar Katsina

-

‘Yan ta’adda a jihar Katsina, sun kai hari inda suka kashe wasu mahalarta ɗaurin aure, tare da sace amarya da wasu mutane 17.

 

Nigerian Post ta bibiyi Rahotan Alfijir Radio da cewa, Harin ya faru ne a yankin Unguwar Nagunda da ke ƙaramar Hukumar Ƙanƙara, washegarin da gwamnatin jihar ta bayyana dalilan shirinta na sakin mutum 70 da ake zargi da laifukan ta’addanci a faɗin jihar.

 

Sai de, daga bisani mutum 8 daga cikin waɗanda aka sace sun samu kuɓuta, inda suka koma wurin iyalansu a ranar Litinin.

 

Kazalika ‘yan bindiga sun kashe wani mutum a ƙauyen Kafa da ke kan babbar hanyar Kankara zuwa Sheme da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara a jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎Wata Mata Ta Rasu A Kano Bisa Zargin Sakacin Likitoci

Wata mata mai suna Aishatu Umar, mazauniyar Jihar Kano, ta rasu da misalin ƙarfe 1:00 na dare bayan shafe tsawon watanni tana fama da matsanancin...

Daga Cikin Kasafin 2026, An Ware Naira Biliyan 1.07 Don Gyaran Gidan Tinubu da Shettima

Gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 1.07 domin gyaran gidajen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima a kasafin kuɗin 2026, lamarin da ya...

Most Popular