HomeSashen Hausa‎Wata Mata Ta Rasu A Kano Bisa Zargin Sakacin Likitoci

‎Wata Mata Ta Rasu A Kano Bisa Zargin Sakacin Likitoci

-

Wata mata mai suna Aishatu Umar, mazauniyar Jihar Kano, ta rasu da misalin ƙarfe 1:00 na dare bayan shafe tsawon watanni tana fama da matsanancin ciwon ciki, sakamakon abin da ake zargin sakacin likitoci yayin aikin tiyata.

Rahotanni sun nuna cewa an yi wa marigayiyar tiyata ne a Abubakar Imam Urology Center a watan Satumba da ya gabata, Bayan kammala tiyatar, Aishatu ta cigaba da fama da matsanancin ciwon ciki, inda duk lokacin da ta koma asibiti, aka rika bata magungunan rage zafi kawai ba tare da gano ainihin matsalar ba.

Bayan shafe kusan watanni huɗu tana wahala, kwana biyu kafin rasuwarta ne aka yi mata gwaje-gwaje da hoton CT scan, inda aka gano cewa an manta almakashi (scissors) a cikin cikinta tun lokacin da aka yi mata tiyatar farko.

Rahotanni sun kara da cewa an shirya a yi mata wata gyaran tiyata domin cire kayan da aka bari a cikinta, sai dai abin takaici, kafin a aiwatar da hakan, marigayiyar ta rasu.

‎Marigayiyar Aishatu Umar ta bar miji da ’ya’ya biyar, lamarin da ya jefa iyalanta da al’umma cikin alhini da jimami.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, inda da dama ke kallon faruwar al’amarin a matsayin sakaci mai tsanani daga bangaren ma’aikatan lafiya, tare da bukatar a hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Al’umma da iyalan marigayiyar sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da hukumomin kula da harkokin lafiya da su gaggauta gudanar da bincike mai zurfi, tare da ɗaukar matakin da ya dace domin tabbatar da adalci ga Aishatu Umar da kuma hana afkuwar irin wannan lamari a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Kanwan Katsina Advocates Establishment of FM Stations Across 3 Senatorial Zones Katsina

The Kanwan Katsina District Head of Ketare, Alhaji Usman Bello Kankara mni, has emphasized the need for continuous training and capacity building for journalists, particularly...

‎Ganduje Ba Shi da Alhakin Sace Dadiyata – Shehu Sani

Tsohon dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ta 8, Shehu Sani, ya karyata zargin da tsohon gwamnan Jihar Kaduna,...

Most Popular