Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya sanar a ranar Alhamis cewa ya yi ritaya daga buga wa ƙasarsa wasa a matakin ƙasa da ƙasa, ya na da shekaru 41.
Ronaldo ya buga wa tawogar Portugal wasanni 234, inda ya zura ƙwallaye 146, wanda hakan ya sanya ya kafa tarihin da ba a samu kamar sa ba a duniya.
A kwanakin baya ne Ronaldo ya fice daga sansanin tawagar ƙasar, inda hakan ya janyo aka dakatar da shi na tsawon kwanaki 30.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Duk da rade-radin cewa yana shirin komawa buga wa ƙasarsa wasa, a yau Alhamis ne Ronaldo, Wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar ya wallafa wani faifan bidiyo a shafinsa na Instagram, inda ya bayyana cewa ya kawo ƙarshen taka leda a tawagar ƙasar Portugal.
“Ya ku al’ummar Portugal, ranar ta zo da zan miƙa rigar mai lamba bakwai ta tawagar ƙasarmu ga waɗanda za su zo nan gaba,” in ji Ronaldo, yayin da ake nuna hotunan wasu muhimman lokutan rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.
