Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja (FCT) ta roƙi mazauna yankin ƙaramar hukumar Bwari da su taimaka wajen gano mahaifiyar wani jariri namiji da ake zargin ta yi watsi da shi.
An gano jaririn cikin mummunan hali, inda aka ruwaito cewa an naɗe shi cikin buhu sannan yana da raunuka a ɗaya daga cikin hannayensa.
NIGERIAN POST ta bibiyi cewa, Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sandan FCT, Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a wani ɗan gajeren bidiyo da ta wallafa a shafin X ranar Laraba.
Ta ce ’yan sanda sun gano jaririn ne ranar Talata, kuma sun kai shi asibiti domin samun kulawar likitoci.
“Mun ɗauko wannan jariri ne a yankin ƙaramar hukumar Bwari. Tun daga safiyar yau muke ƙoƙarin kula da shi saboda ba ya cikin ƙoshin lafiya. Mun same shi cikin mummunan yanayi.”
Ta yi kira ga mazauna Bwari da su taimaka da duk wani bayani da zai iya taimaka wa ’yan sanda wajen gano mahaifiyar jaririn.
