Sunday, November 8, 2026
HomeLabarai’Yansanda Sun Cafke Mutum Biyar Kan Damfarar Naira Miliyan 10 a Katsina

’Yansanda Sun Cafke Mutum Biyar Kan Damfarar Naira Miliyan 10 a Katsina

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta cafke wasu mutum biyar da ake zargi da damfarar kuɗi ta hanyar amfani da asusun bankuna da takardun shaida na bogi, tare da kwato motoci, wayoyin hannu, kuɗaɗe da wasu muhimman kayayyakin da ake zargin sun samo asali daga haramtattun ayyukansu.

Rundunar ta bayyana cewa cafke mutanen na daga cikin nasarorin da ta samu a ci gaba da ƙoƙarin da take yi na yaƙi da laifukan damfara ta yanar gizo da na kuɗi a jihar.

NIGERIAN POST ta bibiyi cewa, hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar ranar 7 ga Nuwamba, 2026, inda ya ce lamarin ya fara ne bayan wani ƙorafi da aka miƙa wa ofishin kwamishinan ’yan sanda a ranar 27 ga Oktoba, 2026, a madadin wani Nasir Dan-Rimi.

Sanarwar ta ce a ranar 10 ga Oktoba, 2026, da misalin ƙarfe 3:45 na yamma, mai ƙorafin ya ba wani Ahmed Abdulhakim, mai shekara 23, kuɗi har Naira miliyan 10 domin ya kammala wani ciniki da yake yi a madadinsa.

Sai dai bayan karɓar kuɗin a cikin asusunsa na banki, Ahmed ya tsere tare da karkatar da kuɗin zuwa amfanin kansa, duk da ƙoƙarin da aka yi na ganin ya mayar da su.

Bayan samun ƙorafin, jami’an bincike na rundunar sun fara gudanar da bincike, inda suka yi nasarar gano wanda ake zargin tare da cafke shi.

A yayin yi masa tambayoyi, Ahmed ya amsa zargin, tare da bayyana cewa kuɗin da ake magana a kai wani ɓangare ne na harkar damfara da suke gudanarwa, inda ya kuma yi ikirarin cewa shi da wanda ya kai ƙorafin duk suna cikin masu damfarar jama’a.

Binciken ya kai jami’an ’yan sandan zuwa wani otal da ake zargin ƙungiyar ke amfani da shi a matsayin maboyarsu, inda suka cafke wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a harkar.

Waɗanda aka cafke su ne Abdulrahman Abdullahi, wanda aka fi sani da Khaila, mai shekara 24, da Mustapha Ayuba, shi ma mai shekara 24.

Rundunar ta ce bincike ya nuna cewa mutanen sun daɗe suna zama a otal ɗin, inda suke amfani da shi a matsayin cibiyar gudanar da ayyukansu na damfara.

Haka kuma, jami’an sun cafke mataimakin manajan otal ɗin, Fahad Ahmad, bisa zargin taimaka wa masu laifi ta hanyar ɓoye su.

An zarge shi da taimaka wa waɗanda ake zargin ta hanyar yawan sauya musu ɗakunan da suke kwana a otal ɗin, domin hana jami’an tsaro gano inda suke da kuma kauce wa cafke su.

Sanarwar ta ƙara da cewa bincike ya gano cewa mutum ukun da ake zargi suna amfani da takardun shaida na bogi, ciki har da lambobin tantance asusun banki (BVN) da na katin shaidar ɗan ƙasa (NIN), domin buɗe asusun bankuna da dama da sunayen ƙarya.

A cewar rundunar, Ahmed yana da BVN da NIN guda uku-uku, waɗanda yake amfani da su wajen gudanar da asusun banki 13.

Haka kuma, Abdulrahman yana da BVN da NIN guda uku-uku da yake amfani da su wajen gudanar da asusun banki shida, yayin da Mustapha shi ma yake da irin waɗannan takardu guda uku-uku, da asusun banki shida.

Rundunar ta ce an buɗe dukkan asusun ne da sunayen ƙarya domin ɓoye ainihin waɗanda suke amfani da su.

Binciken ya kuma gano wasu mutane biyu, Saifullahi Idris da Umar Faruq Bala, waɗanda ake zargin suna taimaka wa ƙungiyar wajen samar da takardun BVN da NIN na bogi.

Haka kuma, Sanarwar ta ce dukkan waɗanda aka cafke sun amsa laifukan da ake zarginsu da aikatawa da kuma irin rawar da suka taka a cikin ƙungiyar.

Daga cikin kayayyakin da jami’an ’yan sanda suka kwato daga hannun waɗanda ake zargin sun hada da;

* Motar Peugeot 206 mai launin toka.

* Farar Motar Mercedes-Benz C300.

* Wayoyin hannu samfurin Samsung Fold, Redmi, iPhone 14 Pro da iPhone 13.

* An kama su da Kuɗi Naira miliyan biyu.

* An kama su dauke da Katunan NIN guda tara, uku daga hannun kowanne daga cikin mutum ukun da ake zargi da jagorantar ayyukan.

* Takardun BVN guda tara da aka yi amfani da sunayen ƙarya wajen samarwa.

* Ƙarin katin NIN guda ɗaya.

* Katunan cire kuɗi na ATM guda tara.

* Katunan SIM guda 14.

* Fakitin katunan SIM guda 12 na kamfanonin sadarwa daban-daban da ake zargin an yi amfani da su wajen aikata laifukan.

Baya ga waɗannan kayayyaki, rundunar ta ce ta kuma samu nasarar sanya takunkumin hana fitar da kuɗi daga wasu asusun bankuna guda biyu da ke ɗauke da Naira miliyan 19 da kuma Naira miliyan uku, wanda jimillarsu ta kai Naira miliyan 22.

Sai dai binciken rundunar ya nuna cewa wanda ya shigar da ƙorafin tun farko, Aminu Nasir Dan-Rimi, tare da wani Surajo Sani Muhammad, su ne ake zargin manyan jagororin ƙungiyar damfarar, kuma a halin yanzu suna can a buya.

Rundunar ta ce tana ci gaba da ƙoƙarin gano inda mutanen suke domin cafke su da gurfanar da su a gaban kotu.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin bisa ƙwarewa da jajircewarsu wajen tabbatar da nasarar cafke waɗanda ake zargin.

Ya kuma jaddada cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen yaƙi da dukkan nau’o’in laifukan damfara ta yanar gizo da sauran laifukan kuɗi a jihar.

Kwamishinan ya gargaɗi masu otal-otal da manajojinsu da su guji ɓoye masu aikata laifuka ko taimaka musu wajen tsere wa jami’an tsaro.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su riƙa kai rahoton duk wani mutum ko ciniki da suka yi zargin akwai wani abu na rashin gaskiya a cikinsa ga hukumomin ’yan sanda domin ɗaukar matakin da ya dace.

DSP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya sanya wa sanarwar hannu a madadin kwamishinan ’yan sandan jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments