Sunday, November 8, 2026
HomeLabaraiRundunar ’Yan Sandan Abuja Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Jami’inta

Rundunar ’Yan Sandan Abuja Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Jami’inta

Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja, ta bayyana alhininta kan rasuwar wani babban jami’inta, CSP Uguemmah Emmanuel, wanda ya kasance jami’in da ke kula da sashen binciken manyan laifuka a ofishin ’yan sanda na Wuse da ke Abuja.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Jami’in ya rasu ne a ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026, lamarin da ya jefa iyalansa, abokansa da abokan aikinsa cikin alhini.

Kakakin rundunar ’yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana rasuwar jami’in a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta tabbatar da cewa rundunar ta yi babban rashi sakamakon mutuwar ɗaya daga cikin manyan jami’anta.

Bayan sanar da rasuwar, kwamishinan ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Ahmed Muhammad Sanusi, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, abokansa da kuma sauran jami’an rundunar da suka yi aiki tare da shi.

Sanusi ya bayyana cewa rundunar na tare da iyalan marigayin a wannan lokaci na jimami, tare da miƙa musu ta’aziyya bisa wannan babban rashi da suka yi.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba iyalan marigayin da sauran waɗanda rasuwar ta shafa ƙarfin zuciya da haƙurin jure wannan babban rashi.

Kwamishinan ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin, Ya jiƙansa da rahama, Ya sanya Aljannar Firdausi ta zama makomarsa.

Rundunar ta kuma bayyana cewa tana tare da iyalan jami’in a wannan lokaci na jimami, tare da fatan samun sauƙin wannan rashi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments