Wani jami’in ’yan sanda da wata mata mai suna Mrs Victoria Abetnigo sun rasa rayukansu a wasu hatsarurrukan ruwa guda biyu da suka faru a Jihar Bayelsa.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Hatsarurrukan sun faru ne a ranakun Alhamis da Asabar a ƙananan hukumomin Brass da Sagbama na jihar.
A hatsarin farko, wani kwale-kwale da ke tafiya daga Yenagoa zuwa Akassa ya kife a yankin ruwan Abedigbene da ke ƙaramar hukumar Brass.
Kwale-kwalen na ɗauke da fasinjoji takwas, inda jami’an rundunar sojin ruwan Najeriya, masu aikin ceto da kuma al’ummar yankin suka yi nasarar kuɓutar da mutum bakwai.
Daga cikin waɗanda aka ceto har da kwamishiniyar kasuwanci da harkokin ciniki ta jihar, Dr Ebiere Jones, da wani jami’in hukumar NSCDC. Sai dai jami’in ɗan sanda da ke cikin kwale-kwalen ya rasu.
Hatsarin na biyu ya faru ne da misalin ƙarfe 5:20 na safe ranar Asabar a gabar ruwan al’ummar Angalabiri da ke ƙaramar hukumar Sagbama.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Musa Mohammed, ya bayyana cewa wani jirgin dakon mai mallakar kamfanin Sterling Global Oil Ltd ya buge wasu ƙananan kwale-kwale yayin da yake tafiya kusa da gabar ruwa.
A sanadiyyar hakan, kwale-kwalen sun lalace, yayin da Victoria Abetnigo, wadda ke cikin ɗaya daga cikinsu, ta samu munanan raunuka.
An garzaya da ita zuwa babban asibitin Ebedeibiri, inda likita ya tabbatar da rasuwarta. An ajiye gawarta a dakin ajiye gawa na Ofoni.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ajao Saka Adewale, ya bayyana alhininsa kan rasuwar mutanen tare da miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalansu.
Ya kuma yaba wa jami’an sojin ruwan Najeriya da masu aikin ceto da sauran al’ummar yankin bisa ƙoƙarin da suka yi na ceto waɗanda suka tsira.
Kwamishinan ya buƙaci masu tukin kwale-kwale da jiragen ruwa su riƙa bin dokokin kiyaye lafiyar masu zirga-zirgar ruwa, tare da guje wa tukin ganganci.
Ya kuma shawarci fasinjoji da su riƙa sanya rigunan kariya daga nutsewa a duk lokacin tafiya ta ruwa.
