Tuesday, November 10, 2026
HomeLabaraiKotu a Borno Ta Yanke Hukuncin Daurin Shekaru 5 Gidan Yari Ga...

Kotu a Borno Ta Yanke Hukuncin Daurin Shekaru 5 Gidan Yari Ga Wani Dan Borno Bisa Safarar Mutane Zuwa Ghana

Wata Babbar Kotun Jihar Borno da ke Maiduguri ta yanke wa wani mutum mai shekaru 52, Goni Bawa Koterema, hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari bisa laifin safarar mutane zuwa kasar Ghana domin tilasta musu aiki.

Hukuncin ya biyo bayan samunsa da laifin safarar wani mutum mai shekaru 33 daga Jihar Borno zuwa Ghana domin cin zarafinsa ta hanyar tilasta masa yin aiki.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin.

Sanarwar ta ce Mai Shari’a M. B. Umar ne ya jagoranci zaman kotun, mai lamba 11, inda aka tabbatar da laifin wanda ake zargin.

NAPTIP ta bayyana cewa laifin ya saɓa wa sashe na 26(1) na dokar hana safarar mutane ta shekarar 2015.

Hukumar ta jaddada aniyarta ta ci gaba da yaƙi da safarar mutane, kare waɗanda abin ya shafa da kuma tabbatar da hukunta masu aikata irin wannan laifi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments