Wasu ’yan bindiga sun Sàcé mutum biyar tare da harbin wasu mutum biyu a wani hari da suka kai yankin Mista Ali da ke Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Maharan sun kai harin ne da dare, inda suka riƙa harbe-harbe, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici.
Dagacin yankin, Danladi Akinja Kasuwa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce maharan sun shiga garin ne suka fara harbe-harbe, lamarin da ya tilasta wa jama’a tserewa domin neman mafaka.
Ya bayyana cewa mutum biyu sun samu raunukan harbin bindiga, kuma an garzaya da su asibiti domin yi musu magani.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun buƙaci a biya kuɗin fansa kafin su saki mutanen da suka sace, sai dai iyalansu ba su biya kuɗin ba zuwa lokacin haɗa rahoton.
Dagacin ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da ceto waɗanda aka sace.
A halin da ake ciki, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Filato, SP Alabo Alfred, bai tabbatar da faruwar harin ba a lokacin haɗa rahoton.
