Friday, November 13, 2026
HomeLabarai’Yan Sanda Sun Ceto Yarínyà Mai Shekara 3, Sun Kama Kanwar Mahaifiyar...

’Yan Sanda Sun Ceto Yarínyà Mai Shekara 3, Sun Kama Kanwar Mahaifiyar ta Kan Zargin Sàcéta a Zamfara

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta ceto wata yarinya mai shekaru uku, Nabila Abdulganiyu, bayan shafe kusan makonni biyu a hannun waɗanda suka yi garkuwa da ita, tare da kama ƙanwar mahaifiyar ta mai shekaru 26 bisa zargin hannu a sace ta.

Rundunar ta ce an sace yarinyar ne a ranar 28 ga Oktoba, 2026, a Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda, inda waɗanda suka sace ta suka nemi kuɗin fansa naira miliyan 10.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Bayan gudanar da bincike, jami’an rundunar sun cafke wadda ake zargi, Saadiya Sahabi, a ranar 10 ga Nuwamba a yankin Bela, Ƙaramar Hukumar Bungudu.

Binciken farko ya nuna cewa wadda ake zargin ƙanwar mahaifiyar yarinyar ce, inda suke da uba ɗaya amma uwa daban. Ta kuma amsa hannu a laifin yayin binciken ’yan sanda.

Rundunar ta bayyana cewa an kai yarinyar asibiti domin duba lafiyarta, kafin a miƙa ta ga iyayenta a ranar 12 ga Nuwamba, 2026.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP A.M. Bello, ya yaba da aikin jami’an da suka gudanar da binciken, tare da tabbatar da cewa bincike na ci gaba domin gano sauran waɗanda ka iya hannu a lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments