An kai hari kan ayarin motocin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, a karamar hukumar Bichi ta Jihar Kano.
NIGERIAN POST ta bibiyi cewa, Lamarin ya faru ne a yayin yaƙin neman zaɓe da tawagar ke gudanarwa domin neman goyon bayan jama’a, bayan kammala ziyara a kananan hukumomin Tofa, Rimin Gado, Kabo, Gwarzo, Shanono da Bagwai.
Kakakin dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Comrade Ibrahim Garba Shuaibu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun samu bayanan sirri kafin isa Bichi cewa wasu mutane sun tare hanya domin hana su gudanar da gangamin siyasa.
Ya ce bayan isarsu garin, sun fara ganin alamun jifa da duwatsu, kafin wasu matasa dauke da muggan makamai su fito su farmaki ayarin motocinsu jim kadan bayan wucewa sakatariyar karamar hukumar.
A cewarsa, harin ya jikkata wasu magoya bayansu tare da lalata motoci da dama.
Shuaibu ya ce da kansa ya ga motoci kusan bakwai da aka farfasa gilashinsu sakamakon harin.
