Monday, November 16, 2026
HomeLabaraiGobara Ta Hallaka Sabbin Ma’aurata Biyu a Filato

Gobara Ta Hallaka Sabbin Ma’aurata Biyu a Filato

Wata gobara ta yi sanadin mutuwar wasu sabbin ma’aurata, Sikiru Habib da matarsa Ramlat Lawan, bayan ta tashi a gidansu da ke Anguwan Miyango, Bukuru, a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu ta Jihar Filato.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:30 na daren Asabar, lokacin da ma’auratan ke barci a cikin ɗakinsu.

Wani maƙwabcinsu, Injiniya Lawal Suleiman, ya bayyana cewa an garzaya da ma’auratan zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) domin ba su kulawar gaggawa.

Ya ce angon ya rasu ne a ranar Lahadi, yayin da amaryarsa ta rasu a ranar Litinin sakamakon raunukan da suka samu.

Rahotanni sun nuna cewa maƙwabta sun yi ƙoƙarin ceto ma’auratan, inda suka fasa taga suka shiga ɗakin bayan ƙofar ta ƙi buɗewa saboda gobarar.

Ana zargin tashin wutar lantarki mai ƙarfi ne ya haddasa gobarar, sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da musabbabin tashin gobarar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments