Al’ummomi da dama a jihar Zamfara na ci gaba da fuskantar matsanancin matsin lamba daga ’yan bindiga, inda ƙananan hukumomin Maradun, Tsafe da Anka suka fi fama da hare-hare, sace mutane, karɓar haraji da tilasta wa jama’a barin gidajensu.
Wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ya nuna cewa mazauna yankunan na rayuwa cikin fargaba, yayin da wasu al’ummomi suka koma ƙarƙashin ikon ’yan bindiga, waɗanda ke karɓar miliyoyin kuɗaɗe kafin su bar mutane su zauna ko su yi noma.
A ƙaramar hukumar Tsafe, mazauna yankin sun bayyana cewa wasu ƙauyuka da dama sun zama babu kowa sakamakon hare-haren ’yan bindiga. Sun ce ana tilasta wa al’ummomi biyan kuɗaɗen haraji da suka kai miliyoyin Naira, tare da tilasta musu yin aikin gonakin ’yan bindigar kafin su kula da nasu gonakin.
Wani mazaunin yankin mai suna Musa Ibrahim ya bayyana cewa ’yan bindiga sun sanya wa wasu ƙauyuka harajin Naira miliyan 10 kowannensu, inda ya ce duk al’ummar da ta gaza biyan kuɗin na fuskantar barazanar korarsu daga gidajensu.
A ƙaramar hukumar Anka kuwa, wani mazaunin yankin ya ce daga cikin ƙauyuka 70 da ke yankin Bagega, guda huɗu ne kawai ke da mazauna, yayin da sauran 66 suka zama babu kowa sakamakon hare-haren.
Ya ƙara da cewa kasuwanni da makarantu da dama sun daina aiki, yayin da wasu gine-ginen makarantu suka koma gidaje ko wuraren ajiye kayayyakin ’yan bindiga.
A ƙaramar hukumar Maradun kuma, an sake samun wani mummunan hari a ranar 7 ga Nuwamba, inda wasu ’yan bindiga suka ƙona gida tare da hallaka mutum 12 daga cikin iyali guda a ƙauyen Gidan Taba.
Rahotanni sun ce waɗanda suka mutu sun haɗa da uba, matansa da ’ya’yansa, bayan maharan sun cinna wa ɗakin da suka ɓuya wuta. Sai dai wata mata ɗaya daga cikin mutanen 13 da suka shiga ɗakin ta samu nasarar tsira.
Rahoton ya kuma bayyana cewa hare-haren sun shafi ƙananan hukumomin Maru, Bukkuyum da Kaura Namoda, inda daruruwan mutane suka tsere daga gidajensu, yayin da wasu matafiya da jami’an tsaro suka rasa rayukansu a hare-haren kwanton ɓauna.
A ɓangaren jami’an tsaro, kwamishinan ’yan sandan jihar Zamfara, CP Ahmad Bello, ya danganta ci gaba da ayyukan ’yan bindigar da yanayin ƙasa, dazuzzuka, tsaunuka da nisan wasu yankuna daga cibiyoyin tsaro.
Ya kuma bayyana cewa wasu mutane na taimaka wa ’yan bindigar da bayanan sirri kan motsin jami’an tsaro, lamarin da ke kawo cikas ga ayyukan jami’an tsaron.
Sai dai wani masani kan harkokin tsaro, Dr. Yahuza Getso, ya danganta matsalar da yaɗuwar makamai, ayyukan haƙar ma’adinai da kuma gazawar hukumomin da abin ya shafa wajen shawo kan matsalar.
Ya ce ana buƙatar inganta haɗin gwiwar al’umma da jami’an tsaro tare da ɗaukar matakan da za su dakile hanyoyin samun kuɗaɗe da makamai na ƙungiyoyin ’yan bindiga.
