Adadin mutanen da suka mutu sakamakon kifewar wani kwale-kwale a jihar Bayelsa ya ƙaru zuwa 29, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da neman sauran waɗanda suka ɓace.
Hatsarin ya faru ne ranar Juma’a, 20 ga Nuwamba, 2026, kusa da garin Oweikorogha da ke ƙaramar hukumar Southern Ijaw, lokacin da kwale-kwalen da ke ɗauke da fasinjoji daga Ayama zuwa Ukubie domin halartar jana’iza ya kife.
Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ne ya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ranar Lahadi, yayin ziyarar da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kai jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa har yanzu ba a gano kwale-kwalen da ya kife ba, kuma akwai fargabar wasu fasinjoji na iya kasancewa a cikinsa.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa kwale-kwalen bai dace da jigilar fasinjoji ba, sannan wurin da aka ɗauko mutanen ba ya cikin wuraren da aka amince da su domin hawa kwale-kwale.
A wani mataki na tallafa wa waɗanda abin ya shafa, Shugaba Bola Tinubu ya amince da bayar da tallafin naira miliyan 250 ga iyalan waɗanda hatsarin ya rutsa da su.
Haka kuma, ya umarci hukumar NEMA da sauran hukumomin gwamnati su taimaka wajen gudanar da aikin ceto da tallafa wa waɗanda suka tsira.
Gwamnatin jihar ta ce za ta ɗauki nauyin kuɗaɗen jinya da abinci ga waɗanda suka tsira daga hatsarin.
