Hukumar Wayar da Al’umma ta Kasa NOA ta shirya muhimmin taron masu ruwa da tsaki a Katsina domin shawo kan matsalolin rashin tsaro a yankunan karkara da kuma fadan da ke tsakanin makiyaya da manoma a fadin jihar.
Taron masu ruwa da tsakin ya gudana ne a sakateriyar Gwamnatin Tarayya dake akan titin dandagoro a cikin birnin Katsina.
Taron dai ya janyo mahalarta daga bangarori daban-daban dasu hada da Hukumomin tsaro, masu rike da sarautun gargajiya, Shuwagabanni al’umma, malaman manyan makarantu da kuma manyan jami’an Gwamnati.
Wannan na cikin tsarin aiwatarwa na kasa na Shirin wanzar da zaman lafiya tsakanin al’ummomi makiyaya da manoma a fadin ƙasar nan.
Tun farko, Daraktan Hukumar, Malam Muntari Lawal Tsagem ya jaddada bukatar da ke akwai na gaggauta yin sasanci tsakanin bangarorin biyu domin samun zaman lafiya mai daurewa a jihar nan.
Ya zayayyano wasu matsalolin da suka shafi rashin tsaro da zaman lafiya da kuma rashin hadin kan ‘yan kasa, inda hakan ke samuwa ta hanyar tashe-tashen hakula tsakanin makiyaya da manoma wanda hakan ke shafar kowane bangaren yankin kasar nan.
A cewar shi, Jihar Katsina na daga cikin jahohi a arewacin kasar nan masu zaman lafiya da albarkatun kasa hadi da noma, inda a halin yanzu yankin ke fama da matsalolin rashin tsaro saboda yawaituwa ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da kuma masu satar dabbobi.
Ya kuma yabawa kokarin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda yana mai bayyana shi a matsayin jajirtattce wajen tabbatar da tsaro a Jihar Katsina, yana mai nuni da cewa a kwanakin nan akayi zaman sasanci tsakanin makiyaya da manoma a wasu Kananan Hukumar dake jihar nan.
Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina data boyi bayan shirin wanzar da zaman lafiya tun daga tushe a yankunan al’umma a fadin jihar nan.