HomeSashen HausaKotu ta yanke wa ɗan Tiktok mai saka rigar mama hukuncin shekara...

Kotu ta yanke wa ɗan Tiktok mai saka rigar mama hukuncin shekara 1 gidan yari

-

Wata Kotu a Kano, ta yanke wa ɗan Tiktok mai saka rigar mama da wanka akan titi hukuncin shekara ɗaya a gidan gyaran hali.

Kotun Majistiri mai lamba 21 dake zamanta a Gyadi-gyadi, karkashin jagorancin mai sharia Hadiza Muhammad Hassan, ta yanke wa matashinnan Umar Hashim Tsulange da ya kware wajan sanya rigar mama, yana wanka a titi hukuncin zaman Gidan Gyaran Hali na shekara 1, ko biyan tarar Naira 80,000.

Freedom Radio ta rawaito cewa kotun ta kuma umarci Tsulangen ya biya Hukumar tace Fina-finai Naira 20,000 ladan wahalar da ta yi.

A ƙarshe, kotun ta ja hankalin Umar din da ya zama matashi na gari, domin ya kyautata gobensa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Masu Ƙwacen Waya Sun Hallaka Ma’aikaciyar Lafiya A Zariya

Wasu da ake zargin masu kwacen waya ne sun kashe ma’aikaciyar jinya a Asibitin Gambo Sawaba da ke Zariya a jihar Kaduna mai suna Hadiza...

Gwamnan Katsina Ya Zama Abin Koyi Ga Sauran Jihohin Najeriya— Inji Kashim Shettima

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya zama abin koyi idan akai duba da...

Most Popular